'Gidan sauro kalilan ake amfani da su a Afrika'

Wani mutum na kwance a gidan sauro mai magani
Image caption Wani mutum na kwance a gidan sauro mai magani

Wata hukuma mai binciken yadda ake kashe kudaden gwamnati a Birtaniya ta ce, gidajen sauro kalilan ne ake amfani da su cikin miliyoyi da kasar ke bayarwa ga kasashen Afrika a matsayin taimako ta na yaki da zazzabin cizon sauro.

Wani bincike ya nuna cewa a duniya baki daya, zazzabin cizon sauron na hallaka mutane 655,000 a kowacce shekara.

Yayin da wasu miliyan 250 ke kwanciya jinya magashiyyan sakamakon kamuwa da cutar.

Kwamitin yace sakamakon bincike a Najeriya da Saliyo da Tanzania ya nuna cewa "kwalliya ba ta biyan kudin sabulu" ga wannan aniya ta gwamnatin Birtaniya game da yaki da zazzabin a nahiyar.

Manufar gwamnatin Birtaniyar dai ita ce kokarin rage yawan mutanen dake mutuwa sakamakon zazzabin na cizon sauro nan da 2015 a kasashe 10 da aka fi samun kamuwa da cutar.

Misali a Najeriya an samu karuwar mutanen da suka mallaki gidajen sauron daga kashi 8 cikin dari, zuwa kashi 41 daga shekara 2008 zuwa 2010.

Sai dai kuma ba a cimma burin da ake da shi ba na ganin an rinka kwantar da kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar a cikin gidajen sauron.

Wannan dalili ne ya sa kwamitin binciken sanya alamar tambaya ga amfanin taimakon da Birtaniyar ke bayarwa ga kasashen.

Kwamitin binciken na Brittaniya ya nuna bukatar sauya halayyar mutane su san muhimmancin amfani da gidajen sauron.

Inda yace daya daga cikin hanyoyin cimma hakan, ita ce ta sanya hukumomin kasashen da ake ba agaji su kirkiro shirin da za a rinka sa ido don tabbatar da an yi amfani da gidajen sauron.

Wani bincike da BBC ta yi ya nuna cewa, talauci na sanya wasu mutane sayar da gidajen sauron da aka ba su kyauta domin kare lafiyar su da ta 'ya'yansu.

Ministan lafiya na Najeriya, Dr Mohammed Ali Pate ya yi kira ga jama'a, su kula da tsaftar muhalli da gidajen sauron da suka saya ko aka ba su taimako.