Yuguda ya koma kungiyar gwamnonin arewa

Image caption Yuguda ya ce bai yi amai ya lashe ba

Gwamnan jihar Bauchi da ke Najeriya ya ce ya koma cikin kungiyar gwamnonin arewacin kasar, bayan da a baya ya janye daga kungiyar sakamakon wani sabani da ya kunno kai bayan zaben shugaban kungiyar gwamnonin kasar a watan Mayu.

Isa Yuguda ya ce ya dawo cikin kungiyar ce bayan wadansu dattijai sun ba shi shawarar yin hakan.

Da ma gwamnan ya fice daga kungiyar ne bayan ya zargi takwarorinsa na arewacin kasar da karya alkawarin da ya ce sun yi cewa za su zabi gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, a lokacin zaben shugaban kungiyar gwamnonin kasar.

A lokacin ya ce ba zai sake shiga kungiyar ba sai takwarorin nasa sun bayyanawa duniya cewa sun saba alkawarin da suka yi.

Sai dai gwamnan ya koma cikin kungiyar ba tare da gwamnonin sun cika sharudan nasa ba.

Kuma da BBC ta tambaye shi ba ya ganin matakin nasa tamkar ya yi amai ya lashe ne, sai ya ce, '' ai dan fulani ba ya yin amai ya lashe''.

Karin bayani