'Yan banga sun fafata da 'yan Boko Haram

An samu asarar rayuka a wata arigamar da aka yi tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da 'yan banga a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, dake arewa maso gabacin Najeriya.

Rahotanni daga birnin sun ce bangarorin biyu sun gwabza ne a ranar Laraba a unguwar da ake zargin cewa 'yan Boko Haram na da karfi sosai.

Mazauna birnin sun ce 'yan bangar suna neman wadanda ake zargin cewa 'yan Boko Haram ne, domin su mika su hannun jami'an tsaro.

To amma sai 'yan Boko Haram su ka farma su, abinda ya kai ga bangarorin biyu su ka yi ta musayar wuta.

Mutane sun ce sun ji karar bindigogi da fashewar abubuwa a lokacin da ake gwabzawar.

Haka kuma rahotanni sun ce an kashe mutane ukku da ake zargi sun sanya hijabi domin su badda kama a lokacin da suka yi kokarin kaiwa wani ofishin 'yan sanda hari a birnin.

Karin bayani