Za a rantsar da sabon shugaban Masar

Image caption Nan gaba kadan ne za a rantsar da shugaban wucin-gadi na Masar

Nan da 'yan sa'oi kadan ne za a rantsar da alkalin babbar kotun kasar Masar, Adli Mansour, a matsayin shugaban wucin-gadi na kasar bayan sojoji sun kawar da shugaban da aka zaba ta turbar dimokaradiyya, Mista Mohammed Morsi.

Ranar Laraba ne dai sojojin suka hambarar da gwamnatin Mista Morsi.

Kakakin jam'iyyar 'yan uwa musulmi, Gehad el-Haddad, ya shaidawa BBC cewa ana tsare da shugaba Morsi da masu bashi shawara a hedikwatar tsaron fadar shugaban kasar.

Ya kara da cewa an hana Mista Morsi yin magana da kasashen duniya.

Tun da fari, shugaban rundunar sojin kasar, Janar Fatta Al-sisi, ya bayyana cewa an soke kundin tsarin mulkin kasar, kuma za a nada sabuwar gwamnati.

Duniya ta yi raddi a kan hambarar da Morsi

Shugabannin kasashen duniya sun mayar da martani game da cire Mista Morsi daga kan mulki.

A martaninsa, shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya yi matukar damuwa da yadda sojin Masar suka cire Mista Morsi, yana mai cewa ya kamata a yi gaggawar kafa gwamnatin dimokaradiyya amma ba wacce shugaba Morsi zai jagoranta ba.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya yi kira ga 'yan kasar Masar su zauna lafiya, kana su tattauna da juna kan yadda za a tabbatar da mulkin dimokaradiyya.

Su ma gwamnatocin Burtaniya, da Jamus, da Saudi Arabia sun nuna matukar damuwarsu game da abubuwan da ke faruwa a Masar.

Karin bayani