Tarayyar Afirka ta dakatar da Masar

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da Masar daga wakilci a cikinta sakamakon kifar da gwamnatin Mohammed Morsi da sojoji suka yi.

A cikin wata sanarwar da ta bayar, kungiyar ta ce ba za a bar Masar ta shiga dukkan wani abu na kungiyar ba har sai ta maido da kundin tsarin mulkin kasar.

Kungiyar ta ce tunbuke Mohammed Morsi ya sabawa tanadin tsarin mulkin.

Haka kuma ta yi kira ga sabbin mahukuntan na Masar su tattauna da dukkanin kungiyoyin siyasar kasar.

Kwamishiniyar kula da harkokin siyasa ta kungiyar Tarayyar Afrikan, Dr Aisha Laraba Abdullahi, ta sheda wa BBC cewa Masar din ta karya dokokin zama cikin kungiyar da aka shimfida.

Ta ce 'yan kasar Masar sun zabi Mr Morsi ne ya shugabance su; kuma bai kamata ba a cire shi har sai wa'adin mulkinsa ya kare.

Sai dai ta ce ba wai kungiyar ta ce dole ne sai Mr Morsi ne kadai za ta yi hulda da shi ba; a'a, ta ce ne sai shugaban da aka zaba ta tabarkin dimukradiyya ne kawai ya kamata ya jagoranci kasar ta Masar.

Ta kuma ce girman kasar Masar din bai hana a hukunta ta ba, tunda ta karya dokar kungiyar.