An kai hari kan jami'an tsaron Masar

Hari a  yankin Gaza
Image caption Hari a yankin Gaza

An kai farmaki kan jami'an tsaron kasar ta Masar a wasu jerin hare-haren roka da bindigogi masu sarrafa kansu, an kuma kashe sojan kasar daya.

Kafafen yada labarai na gwamnatin kasar da jami'an tsaro, sun dora alhakin harin kan 'yan gwagwarmaya musulmi da suka kai hari a kan wajen wani binciken ababan hawa da wani ofishin 'yan sanda da ke kusa da iyaka da Israela da zirin Gaza.

An kuma jikkata wasu sojoji biyyu a hare haren.

Yankin dai ya kasance maras cikakken tsaro da ikon hukuma, tun lokacin da aka hambarar da Shugaba Hosni Mubarak shekaru biyu da suka wuce.