An kashe wasu masu zanga zanga a Masar

An bada rahoton kashe akalla mutane ukku sa'adda sojojin Masar suka bude wuta akan magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi, wadanda ke tattaki zuwa wata cibiyar sojin kasar.

Wakilin BBC na Gabas ta Tsakiya ya ce ya ga sojojin sun yi harbi da farko a sama, kafin sun mayar da bakin bindigogin wajen mutane.

Wani mutum ya fadi a kasa da kayan jikinsa jina-jina.

Kakakin sojin ya musunta cewa sojoji na yin amfani da burussai.

Wakilan BBC sun ce sun ji karar harbe harben bindigogi na fitowa daga bangaren masu zanga zangar ma.

Suna dai tattaki ne zuwa wurin hutawar dakarun dake kare shugaban kasa, wurin da aka yi amannar cewa nan ne ake tsare da Mr Morsi.

Masu zanga zangar suna cikin fushi sosai.

Wani wakilin BBC kuma ya ce a garin Qina, dake kudancin kasar, sojoji sun bude wuta akan masu zanga zangar dake kokarin kutsawa cikin wani ofishin tsaro.

Karin bayani