Masu zanga-zanga da dama sun mutu a Masar

Zanga-zanga a kasar Masar
Image caption Zanga-zanga a kasar Masar

Mummunan fadan da ya rincabe tsakanin magoya bayan hambararren shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi ya haifar da mutuwar mutane da dama.

An dai yi arangama a biranen Alkahira da Askandariya.

Wakilin BBC a dake babban birnin ya ce bangarorin biyu sun rika jifan juna da duwatsu da kwalabe a kan gadar dake kusa da dandalin Tahrir.

Masu zanga-zangar nuna adawa da shugaba Morsi sun rika sowa, lokacin da jami'an soji suka shiga tsakani suna fafarar magoya bayan tsohon shugaban.

Akalla mutane 12 ne suka hallaka a birnin Askandariya, bayan wasu harbe-harbe a lokacin wani gangami.

A baya dai an kashe mutane da dama kusa da sansanin sojin dake birnin Alkahira, inda sojoji suka budewa masu zanga-zangar da ke yunkurin manna hotunan hambararren shugaban kasar a jikin wani shinge wuta.