Ana nuna damuwa kan rikicin Masar

Sojojin Masar
Image caption An zargi sojoji da bude wuta kan masu zanga-zanga

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa kan tashin hankalin da aka samu ranar Juma'a a Masar bayan hambarar da shugaba Muhammad Morsi inda mutane fiye da 30 suka mutu.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta nemi shugabannin Masar da su kawo karshen tashin hankalin.

Shi ma sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira da a kare lafiyar masu zanga-zangar.

A ranar Laraba ne sojoji suka kifar da gwamnatin Mr Morsi bayan zanga-zangar da 'yan adawa suka yi.

Masu goyon Muhammad Morsi na gangami a ranar Asabar a unguwar Nasr da ke birnin Alkahira.

Masu adawa da shi ma sun kira zanga-zanga ranar Lahadi domin kalubalantar kungiyar 'yan uwa Musulmi ta su Mr Morsi.

A yanzu haka dai sojoji na tsare da Muhammad Morsi tare da wasu manyan jami'an kungiyar.

Karin bayani