Abu Qatada yana tsare a gidan yari

Image caption Kotun da aka gurfanar da Abu Qatada

Abu Qatada, malamin addinin musuluncin nan mai kaifin ra'ayi yana fuskantar tuhumar aikata ta'addanci a wata kotun Jordan bayan hukumomin Birtaniya sun maida shi gida yau- an kwashe shekaru takwas ana kai ruwa rana a kokarin maida malamin zuwa kasarsa.

Yanzu haka dai ana tsare da Abu Qatada a wani gidan yari dake wajen birnin Amman.

Cikakken sunan Abu Qatada dai shi ne, Omar Othman, kuma ya tashi ne a kasar Jordan, amma rabonsa da kasar fiye da shekaru ashirin.

Tuni dai wata kotu ta tuhumi Abu Qatada da aikata ta'addanci, kuma rahotanni na cewa, wasu masu fafutukar kare hakkin bil'adama na Jordan ne suka yiwa Abu Qatadan rakiya zuwa gida.

Su dai hukumomin kasar ta Jordan suna tuhumar Abu Qatada ne da hannu a kitsa wasu hare-haren bam a shekarar alif dari tara da casa'in da takwas, da kuma yunkurin kai hari akan wani otel da kuma shirin kai hari akan wasu wuraren ziyarar ibada na Kristoci da kuma wani wuri akan iyakar Isra'ila a fiye da shekaru goma da suka gabata.