Hadarin jirgin sama a San Francisco

Hadarin jirgin saman Korea ta Kudu a San Francisco
Image caption Hadarin jirgin saman Korea ta Kudu a San Francisco

Mutane biyu sun mutu , da dama sun jikkata, a hadarin jirgin saman Korea ta Kudu da ya abku a filin saukar jiragen sama na San Francisco.

Jirgin mai kirar Boeing 777, dauke da fasinjoji kusan dari uku daga birnin Soel kasar Korea ta Kudun yayi abinda mahukunta suka bayyana da ''saukar karfi'' ne.

Shaidu sun ce alamu sun nuna jirgin na cikin hadari lokacin da yake tunkarar filin saukar jiragen saman na San Francisco.

Jirgin dai ya kama da wuta, jim kadan lokacin da ya tunkuyi kasa, bayan da jelarsa ta balle.

Ma'aikatan kashe gobara da masu aikin ceto sun kai dauki a yayinda bakin hayaki daga jirgin ya turnuke.

Ana iya ganin fasinjoji da dama na tsalle suna dira ta hanyar ko kofofin shirin ko ta kwana, suna kaiwa ga tudun mun tsira.

Akasarin fasinjojin sun samu kananan raunuka ne, amma akalla 20 daga cikinsu na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

An bayyana cewa wadanda hadarin ya rutsa da su 'yan kasashen Korea ta Kudu, China, da Amurka ne.

Mahukunta sun ce babu wata alamar da ta danganta hadarin jirgin da ta'addanci, kana babu wata matsala a yanayin sararin samaniyar birnin na San Francisco.

A wata sanarwa da kamfanin zirga-zirgar jiragen saman na Asiana na Kasar Korea ta kudun ya fitar, ya ce zai bada cikakken hadin kai ga masu gudanar da binciken musabbabin hadarin jirgin.