An kashe fiye da mutane 50 a Masar

Hukumomi a kasar Masar sun ce fiye da mutane 50 ne aka kashe yau a birnin Alkahira sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga, wadanda ke adawa da tunbuke Shugaba Muhammed Morsi.

Kungiyar Muslim Brotherhood ta zargi jami'an tsaro da yin kisan gilla, inda ta bukaci Misirawa su yiwa sojojin bore.

Sai dai a taron manema labarai, sojoji da 'yan sanda sun karyata zargin, suna masu cewa sun kare kansu ne bayan da mutane dauke da makamai suka diramma hedikwatar jami'an tsaro na musamman, suna jifa da duwatsu da kuma kwalabe masu petur a ciki.

Kakakin dakarun Masar, Kanar Ahmed Mohammed Ali, ya ce: "Duk da irin matakan da jami'an tsaro suka dauka, mun fuskanci turjiya da matakan harzuka masu zanga-zanga don suyi amfani da rikicin don kaiwa cibiyoyin soji hare-hare".

Karin bayani