Paparoma ya ziyarci Tsibirin Lampedusa

Paparoma Francis a tsibirin Lampedusa
Image caption Paparoma Francis a tsibirin Lampedusa

Paparoma Francis ya koka kan abin da ya kira nuna bambanci a tsakanin al'ummar duniya.

Paparoman ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci tsibirin Lampedusa na Italiya, inda yayi addu'a domin dubban 'yan ci-rani daga nahiyar Afirka, wadanda suka nutse a teku yayin da suke kokarin zuwa Turai.

Bakin haure da dama ne suka nutse a ruwa, maza da mata da kananan yara, a kokarin guje ma wasu abubuwa a kasashensu.

Wannan ce ziyarar farko da Paparoman ya kai a wajen birnin Rome, tun lokacin da aka zabe shi a watan Maris.

A yawancin lokuta a tsibirin Lampedusar ne ake tsare 'yan ci-ranin da ba su da takardu, wadanda suka ketaro Bahar Rum daga yankin arewacin Afirka.