Sakamakon hadarin jirgin Korea ta Kudu ya fito

Jirgin Asiana na kasar Korea ta Kudu
Image caption Jirgin Asiana na kasar Korea ta Kudu

Masu bincike kan hadarin da jirgin saman Korea ta kudu ya yi a filin saukar jiragen San Francisco, sun bayyana sakamakon bincikensu.

Sun ce jirgin da ya yi saukar gaggawa a filin jirgin San Francisco a Amurka, yana tafiya a hankali a hankali ne kasa da yadda ya kamata ya yi sosai, a lokacin da ya ke gab da sauka.

Na'urar tattara bayanai ta jirgin ta nuna cewa matukin jirgin ya yi niyyar fasa sauka, kafin jirgin ya bugi kasa.

Hukumomin kamfanin jirgin na Asiana sun ce matukin kwararre ne sosai, amma kuma bai taba sauka, da irin jirgin kirar Boeing 777 ba, a filin jirgin saman na San Francisco.

Bayanai dai sun ce wadanda hadarin ya rutsa da su 'yan kasashen Korea ta Kudu da China da kuma Amurka ne.