Masar na shirin zabe shekara mai zuwa

Image caption Masar na shirin zabe shekara mai zuwa

Shugaban kasar Masar na rikon kwarya na kokarin kwantar da hankula a kasar, inda ya kudiri aniyar yin zabe a farkon shekara mai zuwa.

Shugaba Adly Mansour ya ce za a yi gyara a kundin tsarin mulkin da 'yan uwa musulmi suka yi, kuma za a yi zaben raba gardama akan sauye-sauyen a watanni hudu.

Sanarwar ta zo ne a lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin sojin kasar da kuma masu marawa hambararren shugaban Mohammed Morsi baya.

Rahotanni na cewa akalla mutane hamsin da daya sun mutu ranar Litinin, lokacin da masu marawa Morsi baya suka yi arangama da sojoji.

Karin bayani