'Yan uwa musulmi sun yi watsi da zabe

Magoya bayan hambararren shugaban Masar, Morsi
Image caption A daren ranar Litinin ne dai shugaban rikon kwarya, Adly Mansour ya sanar da shirin sabon zaben

Manyan jami'an kungiyar 'yan uwa musulmi sun yi watsi da jadawalin sabon zaben da shugaban Masar na rikon kwarya Adly Mansour ya fitar.

Wani kusa a kungiyar, Essam al-Erian yace shirin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar da kuma zabe a shekara mai zuwa, maido da hannun agogo baya ne.

Sojoji sun hambarar da shugaba Morsi a makon jiya, bayan zanga-zangar da aka yi a kasar.

Dokar dai ta zo ne sa'oi bayan kisan mutane 51 a barikin sojoji a Alkahira, inda magoyan Morsi suka ce ana tsare da shi.