Shugaba Jonathan na ziyara a China

Image caption Shugaba Jonathan na ziyara a China

Shugaban Najeriya, Good Luck Jonathan da tawagarsa a ranar Talata za su fara ziyarar kwanaki biyar a kasar Sin, domin kara kulla dangantaka a fannoni daban-daban da suka hada da tsaro da bunkasa tattalin arziki.

Ana sa ran shugabanin kasashen biyu zasu rattaba hannu kan yarjejeniya daban-daban kafin a kammala ziyarar.

Ana fatan dai wannan ziyarar zata kara dankon dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.

A sanarwar da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin 'yada labarai, Reuben Abati ya sawa hannu, ta ce Shugaba Jonathan zai nemi 'yan Kasar Sin su kara zuba jari a aiyukan samar da wutar lantarki a Mambila, da layin dogo na zamani da gina hanyoyi har ma da bunkasa aiyukan noma.

Karin bayani