'Cin hanci na karuwa a kasashen duniya'

Rahotannin cin hanci da rashawa
Image caption Rahotannin shekara-shekara game da cin hanci da rashawa na kungiyar Transparency International

Wani bincike da kungiyar tabbatar da adalci ta Transparency International ta gudanar, ya nuna cewa cin hanci da rashawa na ci gaba da karuwa a kasashe daban-daban na duniya.

Kungiyar ta Transparency ta aiwatar da binciken a kan mutane 114,000 a kasashe 107 na duniya.

Kuma fiye da rabin mutanen da aka ji ra'ayoyinsu a binciken game da cin hanci da rashawar sun ce, lamarin ya munana a shekaru biyu da suka wuce.

Yayin da kashi daya bisa hudu ke cewa sun ba da cin hanci da rashawa ga jami'ai a cikin watanni 12 da suka gabata.

Amma kungiyar ta ce kashi 90 cikin dari na mutanen da aka ji ra'ayoyin nasu, na son a rika daukar kwararan matakai, domin magance matsalar cin hanci da rashawa.

Rahoton dai ya nuna cewa matsalar ta fi kamari ne a tsakanin 'yan sanda da kuma bangaren shari'a.

Haka kuma kasashe takwas cikin goma da suka fi fama da matsalar cin hanci da rashawa matalautan kasashe ne a nahiyar Afrika.