Tsawa ta girgiza birnin Toronto a Canada

Image caption Tsawa ta girgiza birnin Toronto na Canada

Wata tsawa mai karfin gaske ta girgiza birnin Toronto na kasar Canada, inda ta haddasa ambaliyar ruwa da katsewar wutar lantarki.

Fiye da fasinjoji dubu daya ne suka yi cirko-cirko na tsahon sa'o'i da dama, a tashar jirgin kasa,wanda ya tsaya cak saboda ruwan da ya sha kansa har kusan zuwa tagoginsa.

Wani ganau ya bayyana yadda ya ga mutane na barin motocinsu tare da darewa bishiyoyin da ke gefen tashar jirgin, a lokacin da ruwan ya taho gadan-gadan.

An dai katse wasu daga cikin Na'urorin da ke karkashin kasa.

Karin bayani