Apple ya hada baki kan littafin kwamfuta

Littafin da ake wallafa wa a kwamfuta ko ebook
Image caption Littafin da ake wallafa wa a kwamfuta ko ebook

Wata mai shari'a a Amurka ta yanke hukuncin cewa, Apple ya hada baki da wasu mawallafa, wajen sanya farashin litattafan da ake bugawa a kwamfuta.

Mai shari'ar ta Manhattan, Denice Cote ta ce kwamfanin da ya kera iPad "Ya hada baki domin kawo tsaiko a kasuwanci."

Sai dai kakakin kamfanin, Tom Neumayr ya ce Apple zai daukaka kara a kan hukuncin, kuma zai yaki zarge-zarge marasa tushe.

Biyar daga cikin mawallafan da aka shigar da su kara tare da Apple sun riga sun cimma yarjejeniya a wajen kotu, ciki har da Penguin.

Mai shari'ar ta kuma ba da umarnin shigar da wata kara domin tantance barnar da aka samu, tare da dora wa Apple alhakin hakkan.

Sashen shari'a na Amurka ya ce an yi hadin bakin ne domin kalubalantar shagon intanet na sayar da kayayyaki na Amazon, wanda ya yi kakagida kuma yake habaka a kasuwar.

Penguin ya biya dala miliyan 75 a wajen kotu.

Hachette da HarperCollins da kuma Simon da Schuster sun hada asusun dala miliyan 69, domin mayar wa masu hulda da su.

Yayin da kamfanin Macmillan ya biya dala miliyan 26.

Mai shari'a Cote ta ce "Wadanda suka shigar da karar sun nuna cewa mawallafan sun hada baki da juna, wajen kawar da gasar farashin kayyakin da ake sayarwa, domin kara farashin litattafan na kwamfuta. Kuma Apple ya taka rawa sosai wajen aiwatar da hadin bakin."

"Ba domin Apple ya yi hakan ba, da bai yi nasara ba kamar yadda ya faru a shekarar 2010." Inji mai shari'ar.