Barclays ya rufe asusun tura kudi Somalia

barclays
Image caption Bankin Barclays na Birtaniya

A ranar Larabar nan ce Bankin Barclays na Birtaniya yake rufe assusun ajiya fiye da dari daya da ake amfani dasu wajen aika kudade.

Bankin yace ya dauki matakin ne saboda fargabar ana amfani da asusun wajen halasta kudaden haramun.

Kamfanonin aika kudaden dai suna da matukar muhimmanci ga 'yan kasar Somalia, wajen aika kudi gida saboda durkushewar harkokin bankuna a can.

Kamfanoni aika kudade da dama da suka hada da Dahabshiil wanda ya fi kowanne girma, sun ce bankin Barclays ya daga musu kafa na karin wata guda.

Karin bayani