Ana kazamin fada a Homs na Syria

garin Homs na Syria
Image caption garin Homs na Syria

Ana ci gaba da tafka kazamin fada a garin Homs na Syria, yayinda dakarun gwamnati ke kara tunkarar yankuna na karshe dake hannun 'yan tawaye.

Gwamnati ta ce tana kai farmakin ne a kan 'yan hana ruwa gudu na kasashen waje, da kuma 'yan ta'adda na cikin gida.

Kawancen 'yan adawan Syria na SNC ya nemi da a tsagaita bude wuta, yana mai cewa fararen hula na mutuwa sakamkaon karancin magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya.

Wani mai fafutuka ya shaida ma BBC cewa iyalai na zama a yanayi irin na zamanin da, ba ruwan pampo ba wuta. Mayakn 'yan tawaye sun fitar da wani hoton video suna sanye da wasu rigunan da aka yayyabe da bama-bamai suna masu cewa makaman da suka rage masu kenan a halin da ake ciki.