Ministoci biyar sun yi murabus a Morocco

Image caption Mionistoci biyar sun yi murabus a Morocco

Ministoci biyar masu ra'ayin mazan jiya daga jam'iyyar masu kishin Islama a Morocco sun yi murabus daga mukamansu, abin da ya girgiza gwamnatin hadaka ta kasar.

Kakakin jam'iyyar Istiqbal ya ce sun janye goyon bayan da suke ba wa gwamnati, saboda rashin tafiyar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

Ya zama wajibi ga jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayi ta Islamist party of Justice and Development mai mulkin kasar, ta nemi wata jam'iyyar da za su yi hadaka.

Masu nazarin al'amura na ganin yin hakan ne zai sa ta gujewa yin sabon zabe, bayan kwashe kasa da shekaru biyu a kan karagar mulki.

Karin bayani