Majalisar wakilai ta karbe ragamar majalisar Rivers

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta karbe alhakin gudanar da ayyukan Majalisar Dokoki ta Jihar Rivers dake yankin kudu maso kudancin kasar.

Majalisar Wakilan ta yanke shawarar daukar wannan mataki ne, bayan wata muhawara da ta yi a ranar Laraba game da rikicin da ya barke a majalisar dokokin jihar ta Rivers.

A ranar Talata ne rikici ya barke a majalisar jihar, wanda ya kai ga ba hammata iska a lokacin da wasu 'yan majalisar suka yi yunkurin gabatar da kudurin tsige kakakin majalisar.

Majalisar Wakilan ta kuma baiwa Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya umarni, ya nada wa jihar sabon kwamishinan 'yan sanda.

Haka kuma rahotanni daga jihar sun ce an ji karar harbe-harbe a harabar gidan gwamnatin jihar Rivers dake garin Fatakwal, babban birnin jihar.

Ko da yake kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP, Angela Agbeh ta musanta rahotannin.

Wasu na ganin wannan dambarwar cigaba ne na wani takun saka tsakanin masu goyon bayan gwamnan jihar Rotimi Ameachi da kuma masu adawa da shi.