An wanke wanda ake zargi da dana Bam a Boston

 Dzhokhar Tsarnaev  da dan uwansa da aka zarga da dana bam a Boston
Image caption Dzhokhar Tsarnaev da dan uwansa da aka zarga da dana bam a Boston

Wata kotu dake zamanta a Boston a Amurka ta wanke mutumin da ake zargi da ta da bam, a gasar gudun ya da kanin wani a Boston daga laifuffukan da ake tuhumarsa.

Dzhokhar Tsarnaev ya yi magana a kotu a karon farko, tun bayan afkuwar lamarin a watan Aprilun da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku tare da jikkata mutane 260.

Mildred Valverde daya daga cikin wadanda suka ji rauni a lokacin ta ce "Da takaici ace wai ba a same shi da laifi ba, duk da cewa kowa ya san ba haka bane."

Bayan an tashi daga kotun Mr. Tsarnaev wanda ke sanye da rigar fursuna ruwan goro da ankwa a hannunsa, ya sumbaci hannunsa tare da hurawa 'yan uwansa iskar.