Ana tuhumar Karadzic da kisan al'umma

Alkalai dake sauraran daukaka kara a kotun shari'ar laifukan yaki ta duniya dake Hague sun mayar da tuhumar da ake yiwa tsohon jagoran Sabiyawan Bosnia, Radovan Karadzic, na kisan al'umma.

Hakan na nufin cewa an sauya hukuncin farko da ya wanke shi daga zargin jagorantar kisan da kuma cin zarafin wadanda ba Sabiyawa ba a lokacin fara yakin Bosnia.

Kotun ta yi watsi da ikirarin Karadzic cewa bai yi nufin aikata kisan al'umma ba.

Lauyansa, Peter Robinson, ya ce Mr Karadzic zai cigaba da kalubalantar tuhumar.

Yace: "Shugaba Karadzic ya yi bakin cikin wannan hukunci na yau, amma ya na daukar dukkan bayanan da aka yi kuma mun kudiri aniyar gabatar da hujjoji domin kalubalantar ba ma tuhumar da yake fuskanta a yanzu ba kadai; a'a, har ma da tuhumar laifukan yakin."