Paparoma ya tsaurara dokokin hana cin zarafin yara

Paparoma Francis
Image caption Paparoma Francis

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya tsaurara dokokin fadar Vatican akan cin zarafin yara kanana.

Dokar ta hada da abin da fadar Vatican din ta kira fadada fassarar laifukan da suka shafi cin zarafin yara kanana wanda ya hada da aikata lalata da yara da kuma hotunan batsa na yara.

Gyaran ya shafi limaman coci kimanin dubu biyar ko fiye da haka, ya kuma tanadi sallamar wadanda suke aiki a birnin Vatican da aka samu da laifi ko da kuwa an aikata laifin ne a tsallaken iyakokin fadar ta Vatican.