Malala ta yi jawabi mai sosa rai

Image caption Malala Yousefzai

Dalibar nan 'yar kasar Pakistan wacce 'yan Taliban suka harba a bara, Malala Yousefzai, na bukin cikarta shekaru goma sha shida a duniya, tare da yin jawabi ga wani zama na musamman na majalisar dinkin duniya.

Bayan da mahalatar zaman suka mike tsaye don girmamata, Malala ta yi kalamai masu sosa rai game da 'yancin kowanne yaro ya samu ilimi.

Sannan ta yi Allawadai game da hana wasu yaran karatu, inda tace yin hakan nuna son zuciya ne.

Malala ta yi kira ga duniya baki daya ta hadu wajen yaki da jahilci.

An harbi Malala ne a kai da kuma wuyarta bayan da take kampe don samarwa mata ilimi a Pakistan.

Ta ce ta yafewa mutanen da suka kai mata hari.

Karin bayani