Magoya bayan Morsi na shirin zanga-zanga

Image caption magoya bayan Morsi na shirin zanga-zanga

Shugaban Masar, Muhammad Morsi, da 'yan adawa sun yi kiran a fito zanga-zanga a yau juma'a, ya yin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula tun bayan da sojojin kasar suka hambarar da Mr Morsi daga shugabancin kasar.

Jam'iyyar 'yan uwa musulmi ta ci alwashin ci gaba da zanga-zanga har sai an dawo da Morsi mukaminsa, sannan an shirya zanga-zanga a wasu sassan birnin Alkahira.

Suma 'yan adawa sun yi kiran jama'ar su da su fito zanga-zanga a dandalin Tahrir.

Kimanin mutane hamsin ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da suka faru bayan da sojin kasar suka hambarar da tsohon shugaban kasar.

Da tsakar dare kuma masu kishin Islama a yankin Sinai sun hallaka dan sanda guda a kusa da iyakar kasar da Israila.

Karin bayani