Goodluck na kammala ziyarar China

Image caption Goodluck Jonathan na kammala ziyarar China

A yau ne Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, ke kammala ziyararsa ta kwanaki hudu a kasar China.

Tun da farko dai shugaba Jonathan tare da takwaransa Xi Jinping na kasar China sun jagoranci sanya hannu a kan yarjeniyoyin da za su bunkasa cinikayya, da tattalin arziki, da karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin yarjejeniyoyin da Shugabannin suka sawa hannu akwai batun samarda wutar lantarki dubu uku da dari bakwai a Mambila da kuma Zungeru.

'Yan kasar dai sun jima su na fama da karancin wutar lantarki lamarin da yake ci gaba da durkusar da kamfanoni da kuma sanaoin da suka dogara kan wutar lantarki.

Karin bayani