Amurka na fushi da China kan Snowden

Image caption Amurka na fushi da China kan Snowden

Amurka ta nuna takaicin ta akan gazawar kasar Sin ta mika tsohon jami'in leken asiri Edward Snowden.

A wani taron manema labarai a Washington, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka William Burns ya ce abinda China ta yi akan Mr Snowden ya sabawa kiraye kirayen hada karfi da karfe tsakanin kasashen biyu.

Sai dai a na ta bangaren China ta ce gwamnatin Hong-Kong ta bi ka'ida ne wajen tafiyar da lamarin Mr Snowden.

Mr Snowden dai ya gudu zuwa Hong-kong ne bayan ya bankada wani shirin hukumar leken asirin Amurka na tattara bayanan mutane ta waya ko ta internet,sannan an kyale shi ya bar yankin duk kuwa da bukatar da Amurka ta yi na a mika mata shi.

Karin bayani