A saki Mohammed Morsi inji Amurka da Jamus

Sojojin kasar Masar
Image caption Sojojin kasar Masar

Shugabannin rikon kwaryar a Masar, na samun matsin lamba daga kasashen waje, na su sake hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi.

Wannan na zuwa ne bayan da aka shafe wata ranar ana gudanar da zanga-zangar gama-gari a Alkahira babban birnin kasar.

Yayinda magoya baya da masu adawa da Mr Morsi ke bore bisa titunan birnin Alkahira, Amurka ta bi sahun masu neman sulhu ta hanyar diplomasiyya.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki ta ce, Amurka ta goyi bayan kiran da kasar Jamus ta yi na neman a saki Mr Morsi.

Amurkar a baya na kaucewa fitowa fili ta yi kiran da a saki tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi.

Tana dai kira ne ga sojojin kasar Masar da su daina kame membobin kungiyar Muslim Brotherhood ta hanyar da ba bisa doka ba, ba kuma tare da ta danganta hakan da hambararren shugaban ba.

Amurkar dai ta samu wata kafa ne, bayan da kasar Jamus ta yi kiran da a saki Mr Morsi daga daurin talalar da aka yi masa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar, ta yi gargadin cewa anyi amfani da siyasa wajen cafke 'yayan kungiyar 'yan uwa musulmi ne, kuma ta hanyar da bata dace ba, kana zai haifar da koma baya wajen ci gaban harkokin mulkin dimokaradiyyar kasar ta Masar.

Amurkar kuma ta yi kira ga sojojin Masar din da su bi doka da oda wajen tuhumar duk wanda ake tsare da shi.