Harin bam ya kashe mutane 38 a kasar Iraqi

Harin bam a kasar Iraqi
Image caption Harin bam a kasar Iraqi

Jami'ai a kasar Iraqi sun ce an kashe mutane talatin da takwas, a wani harin bam da aka kai wani gidan cin abinci dake birnin Kirkuk na arewacin kasar.

An kuma raunata wasu mutanen da dama a wannan harin, hukumomi na fargabar adadin mutanen da aka kashe zai iya karuwa.

An tayar da bam din ne da Magariba, lokacin da mutane suka cika gidan cin abincin suna buda-baki.

Gabar dake tsakanin 'yan Shi'a da Sunni na Iraqin ta kara tsananta a bana, abinda ya haddasa karuwar tashe-tashen hankula a kasar.

Rahotanni sun ce wannan ya yi sanadin kisan fiye da mutane dubu biyu da dari biyar, hade da mutanen da aka kashe a wannan watan kadai sama da dari biyu da hamsin.