An kama barayin mutane a Jos

Hukumomin tsaro a Jihar Filato dake arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce sun kama wasu gungun mutanen da ake zargi da satar mutane.

Jami'an rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar sun kuma ce sun kubutar da wasu mutane takwas da mutanen suka yi garkuwa da su a wani otel dake Jos, babban birnin jihar.

Rundunar ta ce ta kama masu garkuwa da mutanen ne a wani samame da ta kai a otel din a jiya Juma'a.

A cewar wata sanarwar da babban jami'in watsa labarai na rundunar ya sa wa hannu, barayin mutanen sun sace mutanen ne a wurare daban daban a birnin na Jos, suka kulle su a dakin otel din, suka kuma kira wasu daga cikin 'yan uwan mutanen suna neman kudin fansa.

Daya daga cikin mutanen da aka sacen kafin jami'an tsaro su kubutar da su, Malam Abdussalam Munka'ila, ya ce an sace shi ne a ranar Juma'a.

Rundunar tsaron ta ce yanzu haka an kama mai otel din na Chiwarna da shugaban gungun wadanda ake zargi da satar mutanen da kuma wani mutum guda daga cikin gungun.

Rundunar ta ce ana can ana yi masu tambayoyi, tana mai kari da cewa ta samu nasarar kama mutanen ne sakamkon bayanan sirri da ta samu daga mutanen gari.

Karin bayani