An kira a kama Shugaban Sudan a Najeriya

Masu fafutikar kare hakkin bil'adama a Najeriya sun ce za su garzaya kotu domin neman sammacin kama shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, idan ya kai ziyara a kasar.

Kafar yada labaran gwamnatin Sudan ta ruwaito cewa shugaban zai tashi zuwa Abuja a gobe Lahadi domin halartar taron Kungiyar Tarayyar Afirka (wato AU) akan cututtukan AIDS da tarin fuka da kuma Malaria.

Wannan zai kasance ziyararsa ta farko zuwa Najeriya tun bayan da kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuka ta zarge shi a shekarar 2009 da laifukan yaki a Darfur.

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama mai suna Nigerian Coalition for the ICC ta ce za ta dauki matakin shari'a domin tabbatar da cewa Najeriya ta cika kudirinta.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kama shugaban na Sudan, da zaran ya isa kasar.

Karin bayani