Obama ya yi rokon a kwantar da hankali

Shugaba Obama ya yi kira ga Amerikawa da su kwantar da hankalinsu, su kuma natsu, kwana daya bayan da aka wanke wani mai aikin sa-kai daga tuhumar kashe wani matashi bakar fata a kasar.

Mr Obama yace duk da cewa mutane na da tsauraran ra'ayoyi akan batun, ya kamata su fahimci cewa Amurka kasa ce mai doka da oda. Kuma alkalan da suka yanke hukuncin sun riga sun zartar da hukuncinsu.

A sanarwa da ya bayar, shugaban yace kamata yayi Amerikawa su karrama Trayvon Martin ta hanyar fara tunanen yadda za'a kawo karshen yin amfani da bindigogi wajen tada hankali a kasar.

Wani kwamitin alkalai dai a Amurkan ya wanke mai aikin sa-kan, George Zimmerman, daga tuhumar da ake masa ta kisan matashi bakar fata a watan Fabrairun bara.

George Zimmerman ya bindige Trayvon Martin yayin wata jayayya a birnin Sanford a jihar Florida.

Lauyoyinsa sun ce ya yi harbin ne domin kare kansa.

Kwamitin alkalan mai wakilai mata su shida ya wanke Zimmerman daga dukkan laifuka shida da aka tuhume shi dasu, wadanda suka haifar da muhawara a kasar akan amfani da wariyar jinsi wajen tantance aikata laifi da kuma bukatar adalci a shari'a.

Daya daga cikin lauyoyin George Zimmerman Mark O'mara yace ya yi maraba da hukuncin.

Ya ce: "Babu shakka mun yi farin ciki da wannan hukunci. Dama George Zimmerman bai aikata komai ba face kare kansa da ya yi, na yi murna da alkalan suka gano hakan."

Bada hukuncin wanke shi daga laifin keda wuya sai aka fara samun zanga zangar nuna rashin amincewa da hakan.

Anyi zanga zangar lumana a akalla a birani ukku a California. Masu zanga zangar sun fusata sosai da hukuncin.

Karin bayani