Ban Ki-Moon ya yi tur da harin Darfur

Dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur
Image caption Dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya yi tur da harin da aka kai kan dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun kasar Tanzania bakwai tare da jikkata wasu goma sha bakwai.

Mr Ban din ya bayyana harin a matsayin ta'addanci, kana ya yi kira a gwamnatin Sudan da ta dauki kwakkwaran mataki na hukunta duk wadanda aka samu da aikatawa.

Mai magana da yawun rundunar kiyaye zaman lafiya ta hadin gwiwar kasashen Afirka da Majalisar Dinkin Duniya UNAMID Chris Cycmanick, ya shaidawa BBC cewa wata kungiyar 'yan bindiga ce ta kai hari kan dakarun.

Ya ce sun kai hari kan dakarun dake sintiri kusa da Khor Abeche, yankin arewa maso gabashin Nyala babban birnin kudancin Darfur.

Wannan hari kan dakarun wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniyar a yankin Darfur, shine mafi muni da aka taba samu.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kididdige cewa akalla mutane dubu dari uku ne suka hallaka, yayin da kusan miliyan biyu suka rasa matsugunai, tun lokacin barkewar rikicin yankin Darfur shekaru goma da suka gabata.