An saki wanda ya kashe matashi a Amurka

Alkalai a Amurka sun wanke wani jami'in tsaron sa-kai, George Zimmerman, daga tuhumar da ake masa ta kisan wani yaro bakar fata a watan Fabrairun bara.

George Zimmerman ya bindige yaron ne, Trayvon Martin, yayin wata jayayya a birnin Sanford a Jihar Florida.

Lauyoyinsa sun ce ya yi harbin ne domin kare kansa.

Kwamitin alkalan, mai wakilai mata su shidda, ya wanke Zimmerman daga dukkan laifuka shidda da aka tuhume shi dasu.

Daya daga cikin lauyoyinsa, Mark O'mara, yace ya yi maraba da hukuncin.

Yace: "Babu shakka mun yi farin ciki da wannan hukunci. Da ma George Zimmerman bai aikata komai ba face kare kansa da ya yi; na yi murna da alkalan suka gano hakan."

Zanga zanga da Fargaba

Bayan da kotun ta wanke shi daga tuhumar dai, George Zimmerman ya nuna fargabar fuskatar matsala.

Wani dan uwansa ya ce Zimmerman na fargabar cewa ba zai taba sake samun cikakken 'yancin walwala ba, duk tsawon rayuwarsa.

Dan uwan nasa, Robert, yace George Zimmerman zai rika tafiya yana waiwaye don fargabar cewa za a iya kaima masa farmaki.

Lauyansa ma yace George Zimmerman na iya fuskantar ramuwar gayya, ganin yadda lamarin ya haddasa muhawara sosai kan batun launi fata a kasar.

Batun dai ya jawo muhawara a Amurkan akan amfani da wariyar jinsi wajen tantance aikata laifi da kuma bukatar adalci a shari'a.

Yanke hukuncin wanke shin daga laifin ke da wuya, sai aka fara samun zanga zangar nuna rashin amincewa da hakan.

Anyi zanga zangar lumana a akalla birani ukku a California. Masu zanga zangar sun bayyana fushi sosai akan hukuncin.

Karin bayani