Gawar dan Faransa aka tsinta a Mali - Faransa

Sojojin Faransa a Mali
Image caption Sojojin Faransa a Mali

Da alamun gawar da aka tsinta a arewacin Mali ta bafaranshen nan ne da masu fafutukar Islama suka kama ashekarar 2011, a cewar ma'aikatar wajen Faransa.

Kungiyar Al-Qaida a arewacin Afrika a baya tace ta kashe, Phillipe Verdon a matsayin martani ga shiga yakin Mali da Faransa ta yi.

An dai kama Mr. Verdon da wani Bafaranshe dan kasuwa a garin Hombori dake arewacin kasar.

A ranar Lahadin data wuce ne, shugaban kasar Faransa Francios Hollande ya ce akwai yiwuwar an kashe Mr. Verdon.

Ana dai cigaba da yin gwaje-gwaje a kan gawar da aka tsinta a farkon watan Yulin da muke ciki.

Amma ma'aikatar harkokin wajen Faransar ta ce da alamu gawar Mr. Verdon ce.