Amurka ta ce Masar ta sake samun damar gyara makomarta

Shugaban riko na Masar da Mr Burns
Image caption Shugaban riko na Masar da Mr Burns

Wani wakilin na gwamnatin Amurka, William Burns ya ce hambarar da shugaban Masar Mohammed Morsi da sojoji suka yi, wata dama ce Masar din ta samu ta kyautata makomar ta.

Yayinda yake magana bayan ya gana da shugabannin rikon kwarya na kasar a birnin Alkahira, Mr Burns ya ce yanzu suna da wata dama ta koyon darussa da kuma gyara kura-kuran da aka yi a kasar a cikin shekaru biyu da suka wuce.

Mr Burns ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su nuna juriya da hakuri wajen tunkarar masu zanga-zanga.

An shirya a daren nan magoya bayan jami'yyar Mr Morsi ta 'Yan Uwa Musulmi za su yi zanga-zanga.

Wakilin BBC ya ce ziyarar Mr Burn, wata alama ce dake nuna cewa a shirye gwamnatin Obama take ta yi aiki kafada da kafada da sabuwar gwamnatin Masar din.

Karin bayani