Fashi a teku na karuwa a Afrika ta Yamma

Wata hukumar dake lura da matsalar fashi a teku a duniya ta ce matsalar ta karu sosai a Afrika ta Yamma, duk da cewa an samu saukinta a sauran sassa na duniya.

A rahoton da ta buga a London, hukumar ta ce 'yan fashin sun fito da wasu sabbin hanyoyin fashi a yankin Afrika ta Yamman inda suke satar mutane suna fashin jiragen.

Hukumar kuma ta yi nuni da cewa lamarin ya ma fi tsananta a Najeriya, wadda tace a bana kawai an samu matsalar yin fashi ko kokarin yin sa har sau 22.

Alkalumman na bana sun karu sosai idan aka kwatanta da na shekara ta 2011 lokacin da lamarin ya auku sau shidda kawai.

Wani masanin harkokin tsaro a teku, Aliyu Abdullahi, ya gaya wa BBC cewa rashin kyawawan dokoki akan harkokin safara a teku a Yammacin Afirka da kuma hadin baki tsakanin masu fashin da wasu jami'an gwamnati ne ke haddasa karuwar matsalar.

Yace: "Akwai binciken da ya nuna cewa a wasu lokuttan masu fashi a teku na yin fashin ne da hadin bakin sojojin dake tsaron wajen".