Obama na rokon a kwantar da hankali

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, yayi rokon da a jama'a su kwantar da hankalinsu, kwana guda bayan wanke wani ma'aikacin sa-kai daga laifin kisan wani matashi bakar-fata a watan Fabrairun bara.

Mr Obaman yace duk da cewa mutane na da tsauraran ra'ayoyi akan batun, ya kamata su fahimci cewa Amurka kasa ce mai doka da oda.

Ya kuma ce alkalan da suka yanke hukuncin sun riga sun zartar da hukuncinsu.

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta ce tana gudanar da bincike kan ko za a sake gurfanar da Mr Zimmerman.

Mr Zimmerman ya ce ya dauki wannan mataki ne don kare kansa, a lokacin da suka yi sa-in-sa da matashin Mr Martin a unguwarsu dake jihar Florida a bara.

Wadansu masu zanga-zanga a birnin Newyork sun bayyana matukar damuwarsu game da wanke Mr Zimmerman da aka yi.

Sun bayyana cewa an nuna rashin adalci wajen gudanar da shari'ar.

An dai fara tuhumar George Zimmerman ne, bayan ya harbe wani matashi Trayvon Martins har lahira a garin Sanford dake jihar Florida.

Lauyoyinsa sun yi tankiyar cewa ya dauki matakin ne don kare kansa, lokacin da suka yi jayayya da Mr Martin a Unguwar su a cikin watan Fabrairun bara.