Birtaniya ta yi martani kan El-Bashir

Firai ministan Birtaniya, David Cameron
Image caption Firai ministan Birtaniya, David Cameron

Gwamnatin Birtaniya ta nuna rashin jin dadinta game da matakin da Najeriya ta dauka, na barin shugaban Jamhuriyar Sudan, Omar El-Bashir shiga kasarta.

Birtaniya ta yi nuni da cewa Najeriyar ta san kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ICC, ta ba da sammacin kama shi.

Wannan mataki a cewa gwamnatin Birtaniya zai iya janyo koma-baya ga ayyukan kotun na tabbatar da adalci ga wadanda ake zargin shugaban Sudan din ya cutar da su ta hanyar aikata laifukan yaki.

Wannan furuci na gwamnatin Birtaniya ya zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama ke sukar lamirin Najeriya.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam a kasar sun garzaya Kotu suna neman a ba da damar kame shugaba El-Bashir, a kuma mika shi ga kotun ta ICC.

Shugaba El-Bashir ya isa Najeriya ne a ranar lahadi domin halartar taron koli na kungiyar Tarayyar Afrika AU.

ICC na zarginsa da hannu a laifukan yakin da aka tafka a Dafur.

Najeriyar dai tana daya daga cikin kasashen Afrika 34 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar amincewa da Kotun duniyar.