Yarjejeniyar gwamnatin Columbia da 'yan tawaye

Mr Ivan Marquez
Image caption Mr Ivan Marquez

Babban mai bada shawara kan neman zaman lafiya na kungiyar 'yan tawaye ta FARC a Colombia ya ce ana gab da kawo karshen takaddama tsakaninsu da gwamnati.

An dai shafe kimanin shekaru hamsin ana gwagwarmayar da makamai a kasar.

Babban mai bada shawarar Mr Ivan Marquez ya ce, batun yake-yaken ba zai dawwama ba, akwai yiwuwar a sasantawa daga nan zuwa watan Nuwamba kamar yadda gwamnatin Colombiar ta nema.

Amma kuma ya yi gargadin hadarin dake tattare da azarbabi wajen cimma yarjejeniyar.

Mr Marquz wanda ke halartar shawarwarin da wakilan gwamnatin Colombiar a kasar Cuba ya ce, kungiyar ta masu neman sauyi tana nazarin hanyoyin da za ta jingine gwagwarmayar da makamai ta shiga a dama da ita a harkar siyasa.

Sai dai kuma 'yan kasar Columbia da dama na dari-dari da batun na Mr Ivan.

Sun yi amannar cewa 'yan kungiyar ta FARC na amfani da wannan dama ta tattaunawar zaman lafiyar don su sake hadewa su kuma kara tattara makamai.

Alhali kuwa, cikin watanni takwas din da aka shafe ana zaman tattaunawar, da kuma zagaye goma sha biyu na shawarwarin, gwamnatin Columbiar da kungiyar 'yan tawayen da Farc sun tsaye ne kawai kan kudira daya daga cikin biyar na ajandar zaman, wato batun garanbawul kan batun filaye.

Amma kuma har yanzu ba a tattauna kan muhimman batutuwa kamar makomar 'yan tawayen a fannonin shiga harkokin siyasa, yin adalci ga wadanda rigingimu suka shafa, fataucin miyagu kwayoyi, da mika makamai ba.