An kama jagoran kungiyar Zetas a Mexico

Yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi a Mexico
Image caption Yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi a Mexico

Gwamnatin kasar Mexico ta ce jami'an tsaronta sun kama jagoran daya daga cikin manyan kungiyoyin dillalan miyagun kwayoyi watau Zetas.

Kungiyar ta Zetas na daga cikin kungiyoyi masu aikata miyagun laifukka.

An ba da rahoton cewa an cafke Miguel Angel Trevino ne wanda aka fi sani da Z - 40 a Nuevo Laredo, a wani birni dake arewacin kasar ta Mexico.

Ya karbi Shugabancin kungiyar ne daga mutumen da ya kirkiro ta Heriberto Lazcano, wanda aka harbe har lahira a wata musayar wuta da suka yi da sojoji a shekara ta 2012.

Wasu fandararrun 'yan sandan Mexico ne suka kafa kungiyar, kuma nan da nan ta zamo kungiyar dake tafka ta'asa, da suka hada da kisan gillar bakin haure da aka sato, da kuma na mambobin wasu kungiyoyin da ba su ga-maciji da juna.

An dai jima ana neman shugaban wannan kungiya wato Mr Trevino ruwa a jallo, wanda ya yi kaurin suna wajen aikata laifukan kai muggan hare-hare, fataucin miyagun kwayoyi, halarta kudaden haram.

An kuma same shi da hannu wajen aikata laifukan kai kaddamar da hare-hare, musamman ma na azabtarwa da yin kisan wasu bakin haure Amurkawa kimanin 72 a birnin San Fernando, da kuma yin kisan gilla ga bakin haure fiye da dari biyu bayan shekara guda.

Jami'an tsaron sun taki sa'a ne wajen cafke shi da sanyin safiyar talata, bayan da aka tsegunta musu.

Wannan dai shine kamu mafi girma na jagoran masu fataucin miyagun kwayoyi da aka taba samu a kasar ta Mexico.