Shugaba Omar El-Bashir ya koma Sudan

Shugaban Sidan Omar El-Bashir
Image caption Ministan lafiyan Sudan, Bahar Idris Abu-Garda ya bayyana ziyarar El-Bashir zuwa Najeriya da cewa, tana cike da nasara

Kamfanin dillacin labarai na Sudan ya ce shugaban kasar Omar El-Bashir ya koma gida a yammacin ranar Litinin, bayan halartar taron koli na kungiyar Tarayyar Afrika a Abuja.

A ranar Litinin ne kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC dake zamanta a Hague ta umarci hukumomin Najeriyar da su mika Shugaba El-Bashir ba tare da bata lokaci ba.

Kotun ta jaddada cewa kasar ta rattaba hannu a kan yarjeniyar amincewa da zartar da umarnin kotun tun a shekarar 2001.

Kotun ta ICC dai ta bayar da sammacin kama shugaban na Sudan ne bisa tuhume-tuhumen da suka shafi aikata laifuffukan yaki a Darfur.

A ranar Lahadi Shugaba El-Bashir ya je Najeriyar domin halartar taron kungiyar ta AU, wanda ake karewa a ranar Talata a kan cututtukan HIV/AIDs da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka.

Ziyarar ta shi zuwa Najeriya ta janyo cece-kuce daga ciki da wajen kasar.

Najeriyar dai ta kare matakin da ta dauka na tarbar shugaban na Sudan da cewa ba ziyara ya kawo wa kasar ba, ya zo halartar taron kungiyar Afrika ne, kuma ba ta da hurumin hana wata kasa halartar taron.