An maido da layukan salula a Yobe

Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa an maido da layukan waya a jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar.

Jihar dai na daya daga cikin jihohi ukun da aka sanya wa dokar ta baci a watan Mayu saboda tabarbarewar.

A halin yanzu mutane na iya kiran 'yan uwansu da ke jihar bayan shafe watanni ba tare da sada zumunci ba.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya kafa dokar ta baci a jihohin Adamawa da Yobe da kuma Borno don murkushe ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram.

Karin bayani