An bude taron kungiyar ECOWAS a Abuja

Shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO
Image caption Shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO

Shugabannin kasashen kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma, ECOWAS ko CEDEAO sun fara taron yini biyu a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ana sa ran taron zai tattauna kan batun rikicin siyasa da kuma tsaro a Mali da kuma Guinea Bissau.

Taron zai kuma duba wani daftari a kan Mali wanda mai shiga tsakani a rikicin na Mali a madadin ECOWAS, kuma shugaban Burkina Faso, Blaise Compaore da mataimakinsa shugaba Goodluck Jonathan za su gabatar.

Kasar ta Mali dai na shirin yin zaben shugaban kasa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekarar.