Mutuwar yara 22 ta janyo bore a Indiya

Yara na cin abin rana na kyauta a wata makarantar firamari a Indiya
Image caption Wani jami'i ya shaida wa BBC cewa suna zaton maganin kashe kwari ne ya janyo gubar a shinkafa ko a gayayyaki

An samu mummunan zanga-zanga a jihar Bihar dake Indiya, bayan mutuwar yara 22 tare da jikkatan wasu, a dalilin cin abinci mai guba.

Iyaye da daruruwan mazauna kauyen da lamarin ya faru sun cinna wa motocin 'yan sanda hudu wuta.

Lamarin ya faru ne a wata makarantar gwamnati dake kauyen Masrakh a gundumar Saran.

An dai fara bincike a kai, kuma za a bada diyyar kudin kasar rupees 200,000 ga kowane iyalan yaran da suka mutu.

Shirin bayar da abincin rana kyauta, wani yunkuri ne na bunkasa yawan yaran dake zuwa makaranta a kasar, sai dai a mafi yawancin lokuta ba a tsaftace abincin.

An dai garzaya da yara 28 asibitin garin Chhapra da bashi da nisa da kauyen, yayin da aka kai wasu babban birnin jihar, bayan aukuwar lamarin.

Yara 47 ne dai suka kamu da rashin lafiya a makarantar Firamarin a ranar Talata, bayan sun ci abincin na kyauta.

Sai dai akwai fargabar cewa yawan yaran da suka mutu ka iya karuwa, saboda wasu yaran basu kai shekaru 12 ba, sannan suna cikin mummunan yanayi na rashin lafiya.