Duniya juyi-juyi: Fursunoni sun zama lauyoyi

Fursunoni a Kenya
Image caption Fursunoni a Kenya

A kasar Kenya fursunoni sun koma masu kare 'yan uwansu tare da taimaka musu fita daga kurkuku, bayan sun zama lauyoyi.

A cewar Douglas Owiyo, daya daga cikin fursunonin dake karantar aikin lauya a kurkukun Shimo La Tewa dake Mombasa, "A makon jiya an rage hukuncin da aka yanke wa Abdi na daurin rai da rai zuwa shekaru bakwai. Haka kuma mun taimaka wa wani ya samu nasara a karar da ya daukaka, kuma tuni ya bar gidan kaso."

An horar da Douglas da wadansu da dama aikin lauya a shekarar 2007, kuma sun samu nasarori a kararraki 3,000 da aka daukaka, duk da cewa ba su zama cikakkun lauyoyi ba.

A Kenya, akasarin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka na gurfana a gaban kotu ba tare da lauya ba; Abdi Moka kuma na cikinsu.

A lokacin da ya gurfana a gaban kuliya bisa zargin aikata fashi-da-makami, ba shi da masaniyar ko ya amsa laifin ko kuma a'a, bare ma yadda zai kare kansa.

Hukunci

A Kenya fashi-da-makami na dauke da hukuncin daurin rai da rai ne, kuma kafin ya ankara an zartar da wannan hukuncin a kansa.

Douglas da sauran fursunonin da aka horar a aikin lauya sun rubuta wata takarda, wadda Moka ya gabatar a lokacin sauraron karar da ya daukaka, kuma sun samu nasara.

Alkalin kotun ya amince cewa ya kamata a tuhumi Moka da laifin da bai kai wannan ba a kuma yanke masa hukuncin da bai kai wanda aka yanke masa tsauri ba.

"Na ji kamar zan yi hauka a lokacin da aka yanke mini hukuncin kisa", inji Moka, yana tuna abin da ya faru.

"Amma yanzu, ina da kyakkyawan fata, godiya ta ga wadannan lauyoyin."

Image caption Abdi Moka da wani fursuna a kurkukun Mombasa

Tasiri

Babban alkalin kotun majistire a Mombasa, Stephen Riech, ya amince cewa rashin lauyoyi masu kare wadanda ake zargi na janyo rashin adalci.

Ya kara da cewa ana ganin tasirin wadanda aka horar a aikin lauya idan wanda ke kare kansa ya zo kotu.

"Da zarar sun yi mu'amala da masu aikin lauya, sai ka ga sun san hakkokinsu", inji alkalin.

"Suna tambaya a ba su takardar bayanan masu bayar da shaida, sannan wani lokaci su nemi a dage karar saboda su samu damar shiryawa sosai.

"Na sha jinsu suna yin tambayoyi masu ma'ana ga masu bayar da shaida a kansu."

Kituo Cha Sheria ce kungiyar dake daukar nauyin horar da fursunonin a Kenya.

Wasu lauyoyi ne wadanda suka damu da rashin wakilici ga talakawa suka kafata a shekarar 1973.

Kuma yanzu Kituo Cha Sheria ta bunkasa har ta kai tana duba fannoni da dama na shari'a.

Tana kamfe a kan batutuwa kamar soke hukuncin kisa, wanda har yanzu yake aiki a Kenya, ko da yake babu wanda aka kashe tun shekarar 1987.

Nasara

To menene ya janyo fursunonin suka samu nasarori a shari'u da dama?

Image caption Omondi na gyara bandaki

Sun bayyana cewa suna duba raunin tsarin shari'a su bankado rashin kyakkyawan bincike daga bangaren 'yan sanda da kuma rashin kwarewar wadansu alkalai wajen yanke hukunci.

Ko menene makomar wadanda aka horar bayan sun bar gida kaso?

Dismas Omondi na cikin fursunonin da aka fara horarwa a sherakar 2007.

Bayan shafe shekaru 13 yana jiran hukuncin kisa, ya samu nasara a karar da ya daukaka, kuma an sake shi a shekarar 2010.

Ya samu nasarar wanke wadansu fursunoni 250 da kansa.

Kuma tun bayan sakinsa yana aiki a babbar kotun Mombasa, amma ba a matsayin mai kare masu laifi ba.

Yana wanke bandakuna ne a babbar kotun ta Mombasa.